Za a tattauna matsalar karacin abinci a Nijar

Taswirar Jamhuriyar Nijar
Image caption 'Yan Nijar kimanin miliyan shida ne ke cikin matsalar karancin abinci

A jamhuriyar Nijar, wata tawwaga ta Majalisar Dinkin Duniya da ta hada da mataimakiyar sakataren majalisar mai kula da ayyukan agaji Mrs. Valerie Amos da kuma Daraktan hukumar raya Kasashen duniya Helen Clark ke fara wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu a Kasar.

Tawwagar za ta je ne domin tattaunawa da hukumomin Kasar da kuma kungiyoyi na duniya da ke tallafa wa Kasar ta Nijar game da halin da ake ciki dangane da matsalar karancin abinci da kuma matakan da suka dace a dauka domin shawo kan matsalar.

Wani bincike dai da gwamnatin ta Nijar da abokan arzikinta su ka gudanar, ya nuna cewa 'yan Nijar kimanin miliyan shida ne ke cikin matsalar karancin abincin wanda kuma gwamnatin Kasar ke bukatar agaji domin tallafa musu.

Ana ci gaba da kokawa

Wasu al'umomin yankin Cintabaraden a arewacin jahar Tawa na ci gaba da kokawa dangane da mayuwacin halin da suka shiga sakamakon matsalar tabarbarewar tsaro da ta addabi wasu sassan Najeriya.

Kazalika, al'ummomin yankin na kokawa da jami'an kwastan da suka ce na kawo cikas ga shigo da kayayyakin abinci daga kasar Aljeriya mai iyaka da Nijar din.

Kuma bayanai sun nuna cewa farashin kayayyakin abincin ya yi tashin gwauron zabo.

A yanzu haka buhun gero ya kai jaka 25 na CFA yayin da farashin dabbobi da su ne mazauna yankin ke dogaro da su ya fadi.