Yunwa:Tawagar Majalisar Dinkin Duniya na Nijar

Wani yaro mai dauke da Tamowa a Nijar Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wani yaro mai dauke da Tamowa a Nijar

Wata tawaga ta Majalisar Dinkin Duniya da ta hada da Mataimakiyar Sakataren majalisar mai kula da ayyukan agaji, Valerie Amos da Daraktan Humar Raya Kasashen Duniya, Helen Clark, na Nijar don wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu.

Tawagar ta gana da jami'an gwamnatin kasar A karkashin jagorancin Firayim minista Briji Rafini.

A wajen ganawar, kwararru da jami'an gwamnatin kasar sun yi wa tawagar cikakkun bayanai game da matsalar abincin da nijar din ke fuskanta.

Tawagar ta ce ana bukatar tan dubu 692 na kayan abinci cikin gaggawa

Karin bayani