Ana kara samun matsalar karancin abinci a Nijar

Wani yaro mai dauke da Tamowa a Nijar Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wani yaro mai dauke da Tamowa a Nijar

A yau ne aka shirya wata tawaga ta Majalisar Dinkin Duniya da ta hada da Mataimakiyar Sakataren majalisar mai kula da ayyukan agaji, Valerie Amos da Daraktan Humar Raya Kasashen Duniya, Helen Clark, suke fara wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu a jumhuriyar Nijar.

Tawagar za ta je ne domin tattaunawa da hukumomin kasar da kungiyoyi na duniya da ke tallafa wa Nijar din dangane da matsalar karancin abinci don shawo kan matsalar.

Tuni dai jama'a a jahar Maradi suka fara kokawa da matsalar ta yunwa, wasu ma sun ce ba su da abincin da za su ci.

Haka kuma kananan yara da dama a garin suna kwance a asibiti suna jinyar tamowa sakamakon yunwa .

A kwanakin baya dai Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa kasashen yankin Sahel ciki harda Niger din za su fuskanci matsalar karancin abinci a wannan shekarar, sabilida rashin kyan daminar da aka samu a shekarar da ta gabata.

Karin bayani