Alassane Ouattara ne sabon shugaban ECOWAS

Alassane Ouattara Sabon shugaban ECOWAS Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Alassane Ouattara Sabon shugaban ECOWAS

Kungiyar raya tattalin arzikin Yammacin Afrika ECOWAS ta zabi shugaban kasar Ivory Coast Alassane Ouattara a matsayin sabon shugaban kungiyar.

Wannan dai na zuwa ne shekara guda bayan da ya lashe zaben shugaban kasar da ya haifar da yakin basasa na watanni hudu a kasar.

Ouattara ya lashe zaben na watan Disamban 2010, sai dai shugaban na wancan lokacin Laurent Gbagbo ya ki amincewa ya mika mulki.

Kuma hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kusan 3,000.

A matsayin shugaban ECOWAS, Ouattara zai rinka karbar bakuncin tarurrukan kungiyar, kuma zai samu damar fada aji sosai.

A lokacin da yake kan jagorancin kungiyar, shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, ya samu yabo daga kasashen duniya wajen jagorantar ECOWAS domin matsa lamba kan Mr Gbagbo ya mika iko.

Kungiyar ta ECOWAS mai mambobi 16, ta kuma zabi Desire Ouedraogo, tsohon Fira ministan Burkina Faso a matsayin shugaban Hukumar gudanarwarta.

Ya maye gurbin tsohon ministan harkokin wajen kasar Ghana James Victor Gbeho.

Karin bayani