Alassane Ouattara shi ne sabon shugaban ECOWAS

Alassane Ouattara Sabon shugaban ECOWAS Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Alassane Ouattara Sabon shugaban ECOWAS

Yayin da yau ne shugabannin kasashen kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka, wato ECOWAS, ke kammala taronsu a Abuja, baban birnin Najeriya, wani batu da ya fito fili shi ne irin kalubalen tsaro da wasu daga cikin kasashen kungiyar ke fuskanta.

Wasu daga cikin kasashen na Afurka ta yamman dai na fama da tashe-tashen hankula da kuma tabarbarewar tsaro, lamarin da wasu ke ganin cewa, ya haifar da koma baya ga tattalin arziki da siyasa da kuma zamantakewar kasashen.

A karshen taron na su dai shugabannin kasashen kungiyar ta ECOWAS sun zabi shugaban kasar Kot de Vuwa, Alassane Outtara a matsayin sabon shugaban kungiyar, yayin da Najeriya ta kammala wa'adinta.

Karin bayani