Shugaban kasar Jamus ya yi murabus

Shugaban Jamus Christian Wulff Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mr Christian Wulff ya dade yana fuskantar matsin lamba kan ya yi murabus

Shugaban kasar Jamus Christian Wulff yayi murabus daga kan mukaminsa, kwana guda bayan masu shigar da kasa sun bukaci majalisar dokoki ta janye kariyar da yake da ita daga fuskantar tuhuma.

Wannan mataki dai na da nasaba da badakalar wani bashi.

Mista Wulff dai yace, zai yayi murabus ne saboda cikin 'yan makonnin da suka gabata kimarsa a idon jama'ar kasar ta raunana.

Sai dai kuma yace, yana da karfin gwiwar cewa, duk wani bincike a karshe zai wanke shi daga duk wani zargi.

Tun watanni da dama da suka wuce ne, Christian Wulff ya ke fuskantar matsin lamba akan yayi murabus, saboda kishin-kishin din da aka samu na wani abun kunya da shafi cin hanci da rashawa, wanda ya hada da wata kumbiya-kumbiya ta bashin sayen gida da kuma zargin yadda wasu manyan shugabannin kamfanoni ke daukar dawainiyar hutunsa.

A wani taron manema labarai da aka kira cikin hanzari, shugaban ya bayyana cewar zai sauka daga mukaminsa na shugaban kasa domin ya bayar da damar nada mutumin da zai gaje shi ba tare da bata lokaci ba.

Babban koma baya

"Kasarmu, tarayyar Jamus, ta na bukatar shugaban kasar da zai sadaukar da dukkanin rayuwarsa ga abubuwan da suka shafi kasa da kuma muhimman batutuwan da suka shafi kasashen waje.

Irin abubuwan da ake fuskanta a cikin 'yan kwanaki da makwannin da suka wuce, sun nuna cewar yadda na ke gudanar da aiki na sun yi rauni. A dalilin haka, ba za ta yiwu in gudanar da aikace-aikacen da suka rataya a wuyan shugaba a ciki da wajen kasa ba".

A ranar Alhamis ne masu gabatar da kara a Hanover suka bukaci majalissar dokoki da ta cire kariyar da Mr Christian Wullf ya ke da ita, domin samun damar kaddamar da bincike akan ko ya tafka wani babban laifi, matakin da ba'a taba daukar irinsa ba akan wani shugaba na kasar Jamus.

Murabus da Mr Wullf yayi, wani babban koma baya ne ga Shugabar gwamnati Angele Merkel, wadda tuni ta soke wata ziyara da ta shirya kaiwa zuwa Italiya, inda ta shaida wa manema labarai cewar ta yi matukar takaicin wannan shawara da shugaban ya yanke.

A yanzu dai akwai babban kalubalen da ke fuskantar Mrs Merkel na samun sabon shugaba, ta kuma bayyana cewar Jam'iyyun da ke cikin gwamnatin gamin-gambizar kasar a yanzu za su fara tuntubar juna domin samun mutumin da zai gaji Mr Christian Wullf.

Karin bayani