Ana zargin Tariq al - Hashimi da hannu a hare- haren Iraqi

Mataimakin Shugaban Kasar Iraqi Tariq al-Hashimi Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ana zargin Tariq al- Hashimi da hannu a hare- haren da ake kaiwa jami'an tsaro

Wani kwamitin bincike a Iraqi ya goyi bayan zargin da aka yi cewar Mataimakin Shugaban Kasar dan Sunni Tariq al-Hashimi ne ke shirya makarkashiyar hare-hare da dama da ake kai wa jami'an tsaro da masu ziyarar Ibada 'yan Shi'a.

Firayim Ministan Kasar dan Shi'a Nouri al- Maliki ne ya ba da umarnin a kame mataimakin Shugaban Kasar tun cikin watan Disambar bara, lamarin da ya haddasa hatsaniyar siyasa tsakanin 'yan Sunnin da kuma 'yan Shi'a.

Kwamitin mai Alkalai tara wanda kotun kolin Kasar ta kafa, ya ce wasu kungiyoyin 'yan bindiga da ke kashe jama'a a karkashin jagorancin Mr. Hashimi ne su ka rinka kai hare-haren tun shekaru da dama da su ka gabata.

Karin bayani