Cuwa-cuwar takardun lamuni na Amurka

Akwatin da ke dauke da takardun lamunin na bogi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Akwatin da ke dauke da takardun lamunin na bogi

'Yan sanda a Italiya sun ce sun kame wadansu takardun lamuni na Amurka na bogi, wadanda kimar su ta kai dala tiriliyan shida, a abin da aka yi amanna cewa shi ne hada-hadar takardun bogi mafi girma a tarihi.

Kimar takardun lamunin dai ta kai kusan rabin ilahirin bashin da ake bin kasar Amurka.

'Yan sanda sun ce an boye takardun lamunin na bogi ne a cikin wadansu akwatuna guda uku a birnin Zurich na kasar Switzerland.

Ya zuwa yanzu dai an kama mutane takwas dangane da al’amarin.