Shagulgulan cika shekara guda da juyin- juya hali a Libya

Tutar Libya Hakkin mallakar hoto reuters
Image caption Ana gudanar da shagulgulan cika shekara da juyin- juya hali a Libya

'Yan Libya na gudanar da shagulgulan cika shekara guda da juyin-juya halin da ya hambarar da Marigayi Kanal Mu'ammar Gaddafi daga kan karagar mulki.

An shirya bukukuwan ne a garuruwa da birane a duk fadin Kasar.

An kafa turakun bincike na jami'an tsaro a Tripoli babban birnn Kasar don kawar da duk wani abin da zai kawo cikas ga shagulgulan.

Wani mazaunin birnin Benghazi ya shaidawa BBC cewar bai taba tunanin za a samu sauyin da aka samu a shekara guda da ta wuce ba.

To, amma a baya-bayan nan an samu karuwar tashe-tashen hankula a Kasar, a yayinda gwamnatin rikon-kwaryar Kasar ke gwagwarmaya da mayakan sa- kai wadanda suka taimaka wajen hambarar da Shugaba Gaddafi.

Karin bayani