Yawan 'yan gudun hijirar Mali ya rubanya

'Yan gudun hijirar Mali Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu daga cikin 'yan gudun hijirar Mali a Yammacin Nijar

Majalisar Dinkin Duniya ta ce adadin ’yan kasar Mali wadanda ke gudun hijira zuwa kasashen da ke makwabtaka da su don gujewa fada tsakanin ’yan tawaye Abzinawa da sojin gwamnatin kasar ya rubanya a cikin kwanaki goman da suka wuce.

Yan gudun hijirar fiye da dubu arba'in da hudu ne suka ketara zuwa kasashen Mauritaniya da Nijar da Burkin Faso, inda a halin yanzu Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ke yi musu rajista.

Kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Amnesty International ta bayyana fadan, wanda ya barke a watan Janairu, da cewa shi ne bala’i mafi muni a kasar ta Mali a cikin shekaru ashirin.

Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Yammacin Afirka, ECOWAS ko CEDEAO, ta yi Allah-wadai da harin da ’yan tawayen suka kaddamar.

Wakilin BBC a Yammacin Afirka ya ce yanzu kura ta dan lafa a yankin.

Karin bayani