Matsalar karancin abinci a Nijar

Valerie Amos Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Valerie Amos

Tawagar Majalisar Dinkin Duniya karkashin jagorancin mataimakiyar sakatare janar, mai kula da ayyukan agaji, Valerie Amos a yau ta ziyarci yankin Tillaberi, daya daga cikin yankunan dake fama da matsalar karancin abinci a jumhuriyar Nijar.

Tawagar ta je yankin ne domin duba yadda ake tafiyar da wasu ayyukan tallafi da majalisar dinkin duniya ke gudanarwa da suka shafi noman rani da kula da yaran dake fama da tamowa.

A jiya ne dai hukumomin na Nijar suka bayyanawa tawagar ta majalisar dinkin duniya irin matakan da suke dauka domin shawo kan matsalar karancin abincin a kasar.

Karin bayani