Zauren Majalisar dinkin duniya ya amince da kuduri akan Syria

Mr. Ban Ki Moon, babban sakataren majalisar dinkin duniya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Babban zauren majalisar dinkin duniya ya yi Allah wa dai da gwamnatin Syria

Babban zauren majalisar dinkin duniya ya amince da wani kuduri na Kasashen larabawa wanda ya yi Allah wa dai da jinin da gwamnatin Syria ke zubarwa.

Kudurin wanda ba lallai a yi amfani da shi ba, ya kuma yi kira ga Shugaba Assad ya sauka daga karagar mulki.

Wakilai dari da talatin da bakwai ne su ka goyi bayan kudurin, wasu kuma goma sha-biyu su ka nuna rashin amincewa da kuma goma sha-bakwai da ba su halarci zaman majalisar ba.

Rasha da China suna cikin Kasashen da su ka nuna rashin amincewa, kamar yadda su ka hau kujerar naki dangane da kudurin kwamitin sulhu na Majalisar dinkin duniyar makonni biyu da suka gabata.

Karin bayani