Amurka ta ce Iran ta shirya shiga tattaunawa

Catherine Ashton da Hillary Clinton Hakkin mallakar hoto a
Image caption Catherine Ashton da Hillary Clinton

Kasar Amurka da Kungiyar Tarayyar Turai sun ce kasarIrana shirye take ta sake komawa tattaunawa akanshirin nan nata na Nukiliya.

Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka, Hillary Clinton, da babbar jami’a mai kula da harkokin waje a Tarayyar Turai, Catherine Ashton, sun ce suna da kwarin gwiwar cewa za a sake komawa tattaunawa da kasar Iran a kan shirin nata na Nukiliya.

Hillary Clinton ta ce wajibi ne kasashe masu karfin fada-a-ji su tabbatar da cewaIrandin ta ci gaba da tattaunawar har sai ta kai ga amincewa da kaidojin kasa da kasa.

“Kasashe shida da kuma sauran kasashen duniya sun jima suna zuba ido su ga kasar taIranta nuna shirinta na hawa teburin tattaunawa”, in ji Misis Clinton.

Karin bayani