Kashe-kashe sun ragu a Mexico -Calderon

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Felipe Calderon

Shugaba Felipe Calderon na Mexico ya ce yawan kashe-kashen da ake yi a birnin Ciudad Juarez wanda ya yi kaurin suna wajen tashe-tashen hankula ya ragu da kusan rabi tun bayan da ya kai kololuwa a shekarar 2010, shekarar da aka kashe mutane fiye da dubu uku.

Mista Calderon ya ce samar da ayyukan yi ya taka muhimmiyar rawa wajen rage tashe-tashen hankulan.

Sai dai masu sharhi kan harkokin tsaro sun ce mai yiwuwa galabar da daya daga cikin kugiyoyin masu fataucin miyagun kwayoyi ta yi kan abokiyar hamayyarta ne ya sa aka samu raguwar kashe-kashe a yankin.

Akasarin kashe-kashen dai sun auku ne sakamakon ba ta-kashin da gungu-gungun masu safarar miyagun kwayoyi wadanda ba sa ga-maciji da juna ke yi.

Karin bayani