An dakatar da wallafa rahoto kan murar tsuntsaye

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu binkice suna gwaji kan cutar murar tsuntsaye

Hukumar Lafiya ta duniya, WHO, ta ba da umurnin dakatar da wallafa sakamakon wani sabon bincike a kan murar tsuntsaye har sai illa ma sha Allahu, saboda fargabar 'yan ta'adda ka iya amfani da shi su haddasa annoba.

Wani taron masana harkar lafiyar al'umma ya amince a wallafa sakamakon gaba dayansa nan gaba.

Ron Fouchier ya jagoranci wasu daga cikin masanan da suka gudanar da binciken:

''Ra'ayin daukacin wadanda suka taru a nan shi ne akwai yiwuwar amfani da kwayoyin da ke haddasa murar tsuntsaye ko ma wasu nau'uka na mura don aikata ta'addanci, amma hadarin yin hakan takaitacce ne matuka''.

Masu binciken sun ce wallafa sakamakon zai taimaka wajen samar da magungunan cutar, sai dai kuma fargabar jami'an tsaro ita ce sanin hanyoyin yada cutar a tsakanin al'umma ka iya zama wani makamin kare-dangi a hannun 'yan ta'adda.

Karin bayani