Rikici ya shafi kokarin China a Syria

Zhain Jun Wakilin China a Syria
Image caption Zhain Jun Wakilin China a Syria

Mummunan rikici ya barke a Damascus, babban birnin Syria, inda wata tawagar diplomasiyya daga kasar China ke kokarin sasanta tsakanin Shugaba Assad da abokan hamayyarsa, masu zanga zanga.

Jana'izar wasu masu zanga zanga da aka kashe jiya a yammacin Damascus ta rikide zuwa daya daga cikin manyan zanga zangar da aka taba gani a birnin.

Masu fafutuka sun ce an kashe akalla mutun daya a lokacin da dakarun tsaro suka bude wuta.

A waje daya kuma wani wakilin gwamnatin China ya yi kira ga 'yan tawaye da dakarun gwamnatin Syrian da su dakatar da rikicin.

Zhai Jun ya ce, gwamnatin China na goyan bayan shirye-shiryen gwamnatin Syria na yin kuri'ar jin ra'ayin jama'a game da sauye sauyen da zaa yiwa kundin tsarin mulkin kasar.

Karin bayani