'Yan adawa sun yi watsi da zaben Sakkwato

Image caption Shugaban Hukumar zaben Najeriya, Attahiru Jega

Jam'iyyun adawa a jihar Sakkwato ta Najeriya sun yi watsi da sakamakon zaben da aka gudanar a jihar ranar Asabar, inda aka ayyana Aliyu Magatakarda Wamakko a matsayin wanda ya lashe shi.

Dan takarar Jama'iyyar adawa ta ANPP Alhaji Yusha'u Ahmad ne kuma ya zo na biyu.

Sai dai Alhaji Yusha'u Ahmad ya ce an tafka magudi a zaben:

''Abin da ya faru a Sakkwato ba zabe ba ne...an zo ranar zabe inda ake ganin ANPP ke kan gaba za a sa matasa su doki mutane, su dauke akwatin zabe, sannan su watsa wurin''.

Ya yi kira ga hukumar zabe da ta sake gudanar da zabe, sannan ta tabbatar ta yi wa kowane dan takara adalci.

Gwamna Aliyu Magatakarda Wamakko ya ce baya shakkar duk wanda zai kalubalanci sakamakon zaben a kotu.

Karin bayani