Shugabannin Afirka sun gudanar da taron koli

Hakkin mallakar hoto
Image caption Dakin taron shugabannin Afirka

Shugabannin kasashen Tarayyar Afirka sun gudanar da taron koli na farko tun bayan da Shugaba Boni Yayi na Jamhuriyar Benin ya zama shugaban kungiyar a watan da ya gabata.

Yayin taron, Mista Yayi ya yi jawabi a kan al'amuran tsaro, ciki har da tashin hankalin da ya barke kwanan nan a Mali, da karuwar fashi a tekun Yammacin Afirka, da kuma barazanar kungiyoyin mayakan sa-kai irin su Boko Haram a Najeriya.

An dai ba da sanarwar cewa Mista Yayi zai ziyarci wasu kasashen da ake fama da rikice-rikice a Afirka ciki har da Sudan da Sudan ta Kudu, da Mali da Libya, don tattaunawa kai-tsaye da wadanda abin ya shafa.

ECOWAS ta zabi Ouattara

A ranar Alhamis ne ita ma Kungiyar raya tattalin arzikin Yammacin Afrika ECOWAS ta zabi shugaban kasar Ivory Coast Alassane Ouattara a matsayin sabon shugaban kungiyar.

Wannan dai na zuwa ne shekara guda bayan da ya lashe zaben shugaban kasar da ya haifar da yakin basasa na watanni hudu a kasar.

A matsayin shugaban ECOWAS, Ouattara zai rinka karbar bakuncin tarurrukan kungiyar, kuma zai samu damar fada aji sosai.

Karin bayani