Masar ta janye jakadanta daga Damascus

Yantawayen Syria Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yantawayen Syria

Kasar Masar ta bayyana cewar za ta janye jakadanta daga Damascus yayinda matsi ke kara karuwa game da tashin hankali a Syria.

Wannan ne dai mataki na baya bayan nan a mayar da Syria saniyar waren da kasashen duniya ke yi.

Kasar Masar ita ce kasa ta baya baya a jerin kasashenLarabawan da suka janye jakadunsu daga Damascus, don nuna rashin amincewa da matakin Gwamnatin Syria a kan masu zanga zanga.

A lokacin da kishin kasashen Larabawa ke ka, shekaru hamshin da suka wuce, kasashen 2 sun taba hadewa ta gajeren lokaci a karkashin ikon Gamal Abdul Nasser.

Haka kuma yunkurin yana nuni da matsin da jama'a ke wa gwamnatin ta Masar na ta dauki kwakwkwaran matsayi.

An dai gudanar da jerin zanga zanga a Alkahira a wajen Ofishin Jakadancin Syriar.

A wani lokaci ma masu zanga zanga har dan samun damar shiga cikin ginin suka yi.

Masu zanga zangar da kuma yan kungiyar yan uwa Musulmi, jama'iya mafi girma a majalisar dokoki, sun bukaci ma da a kori Jakadan Syria a Masar , to amma kawo yanzu hakan ba ta faru ba.

Karin bayani