An kashe mutane 30 a garin Maiduguri

Jami'an tsaro
Image caption An dai tsaurara matakan tsaro a ko'ina a birnin na Maiduguri

Rahotanni daga birnin Maiduguri a jihar Borno da ke Arewacin Najeriya na cewa kimanin mutane 30 ne suka rasa rayukansu a sakamakon harin da 'yan bindiga suka kai a kasuwar Baga, sai dai jami'an tsaro sun musanta adadin.

Wani da ya shaida lamarin ya tabbatarwa da BBC cewa ya ga motocin akori-kura kirarar kanta guda uku ko wacce da gawarwaki akalla Goma.

Sai dai rundunar wanzar da zaman lafiya ta JTF ta ce mutane takwas ne kawai suka mutu.

Wannan lamarin dai ya faru ne bayan harin da aka kai a kasuwar a safiyar ranar Litinin.

Kakakin rundunar Laftanal Kanal Muhammad Hasan Ifeji, ya shaida wa BBC cewa duka mutane takwas din da suka mutu 'yan'yan kungiyar Boko Haram ne.

"Babu koda farar hula daya da ya rasa ransa a harin," kamar yadda Laftanal Kanal Muhammad ya ce.

Ya kara da cewa jami'an rundunar sun kuma kwance bama- bomai uku tare da samun abubuwan fashewa da dama.

Mazauna birnin Legas ma....

Birinin na Maiduguri dai dake arewa maso gabashin kasar, nan ne hedkwatar kungiyar ta Boko Haram - sai dai a baya-bayan nan kungiyar na fadada ayyukanta zuwa wasu sassan kasar.

Yanzu haka mazauna tsakiyar birnin lagos na zaman dardar a sakamakon wata musayar wuta da akayi tsakanin bangarorin dake goyon bayan masu takaddamar shugabancin kungiyar direbobi ta NURTW a Agarawu da Saleko.

Rahotannin da BBC ta samu sun tabbatar da kashe mutum hudu tare da jikkata wasu da dama.

Hakazalika an Lalata motoci kimanin 20 tare da kona wani gida Hawa daya.

'Yan sanda dai sun tabbatar da lamarin amma sun ce, sun tsananta matakan tsaro dan kaucewa sake aukuwar wani rikicin.

Rikicin na yau dai ya samo asali ne daga ci gaba da wata takaddamar shugabancin kungiyar direbobi ta NUTRW.

Karin bayani