Za'a ba Girka tallafin ceto tattalin arzukinta

Masu zanga zanga a Girka
Image caption Masu zanga zanga a Girka

Ministocin kasashen dake amfani da kudin euro na ganawa a Brussels don yanke hukuncin amincewa da sabon shirin ceto tattalin arzikin Girka.

Shirin zai samarwa kasar fiye da dala biliyan dari da saba'in.

Inda kuma za'a yafe mata wasu dumbin basussukan da suka kai biliyoyin euro.

Jean Claude Juncker shugaban kungiyar tarayyar Turai yace ba bukatar wani bane, a fidda Girka daga kungiyar kasashen dake amafani da kudin euro, hakan zai zamo wani mataki mara kyau na warware matsalar Girka.

Ana dai samun tsaikon bada wannan kashi na bashin ne saboda kokarin da ake yi domin tabbatar da cewa, Girka ta aiwatar da tsauraran matakan tsuke bakin aljihu.

Karin bayani