Bullar zazzabin Lassa a jahar Rivers

Taswirar Najeriya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Taswirar Najeriya

An sami bullar cutar zazzabin Lassa a jihar Rivers dake kudu maso kudancin Najeriya.

Bincike ya nuna cewa, an gano bullar cutar ne, yayin da wata malamar asibitin koyarwa na jami'ar Fatakwal ta kamu da zazzabin, wanda kuma ya zama ajalinta.

Daga bisani kuma an gano wasu mutanen da suka kamu da cutar .

Alkaluma sun nuna cewa, mutane fiye da dubu 300 ne kan kamu da zazzabin Lassar a kowace shekara a duniya.

Ana daukar cutar ce daga beraye.

A cewar bayyanai, an fara samun bullar cutar ne a kauyen Lassa dake jihar Borno, a arewacin Najeriya, shekaru fiye da hamsin da suka gabata.

Karin bayani