Red Cross na neman a tsagaita wuta a Syria

Red Cross na neman a tsagaita wuta a Syria Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Fada dai ya tsananta tsakanin 'yan tawaye da kuma dakarun Syria

Kungiyar bada agaji ta Red Cross ICC, ta ce tana kokarin shiga tsakanin gwamnati da 'yan adawar kasar Syria, saboda a samu damar isar da kayan agaji ga yankunan da fadan da ake yi ya fi shafa.

Wata mai magana da yawun kungiyar ta Red Cross a birnin Geneva ta fadawa BBC cewa:

"Kungiyar na duba yiwuwar amfani da hanyoyi da dama da suka hada da neman a tsagaita wuta, domin a samu damar isar da kayan agaji da ake matukar bukata a wasu sassan kasar ta Syria".

Kungiyar ta Red Cross ita kadai ce kungiyar agaji ta duniya da take aiki a yanzu a kasar syria, sai dai yayin da tashin hankalin ya ke dada zafafa a 'yan makwannin nan, ita ma tana fuskantar matsaloli wajen isa ga yankunan da rikicin da ake yi ya fi kamari.

Sai dai a yanzu kungiyar ta Red Cross ta ce tana tattaunawa da sojojin gwamnatin Syria da kuma dakarun 'yan tawaye, a wani kokari na samo hanyar da za ta isar da taimakon jin kai da ake matukar bukata cikin gaggawa.

Amma Red Cross ta ce ba za ta yi karin bayani kan tattaunawar ba, sai dai sun tabbatar da cewa, daya daga cikin batutuwan da ake tattaunawa shi ne yiwuwar tsagaita bude wuta, don baiwa motocin daukar marasa lafiya su shiga su kwaso wadanda suka samu rauni.

Wannan dai ya fito da irin damuwar da kungiyar ke da ita game da tashe-tashen hankulan da ake fama da shi a Syria, da kuma yawan fararen hular da lamarin ke shafa.

Karin bayani