Taron sasantawa tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu

Image caption Shugaban kasar Sudan Omar el-Bashir

Wasu kungiyoyin kabilu daga Sudan da Sudan ta Kudu sun fara wani taron samar da zaman lafiya a tsakanin kabilun.

Hakan na faruwa ne a yayin da ake ci gaba da tayar da jijiyoyin wuya tsakanin kasashen a kan kudin hayar bututun man fetur.

'Yan kabilar Misseriya da ke kasar Sudan za su tattauna da 'yan kabilar Dinka Malwal na kasar Sudan ta Kudu a kan yadda kaurar da su kan yi duk shekara zuwa yankin da a yanzu ya zama sudan ta Kudu za ta rika kasancewa.

Tattaunawa tsakanin kabilun biyu, wadanda a tarihi ba sa ga-maciji-da-juna, za ta kuma tabo batun diyya a kan shanun da aka kashe ko aka sace a baya.

Jagororin kabilun biyu sun ce ba za su bari takaddamar da ke tsakanin kasashensu ta hana su cimma yarjejeniya ba.

Karin bayani