An zargi sojojin Amurka da kona Alkur'ani

An zargi sojojin Amurka da kona Alkur'ani Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sojojin Amurka sun nuna matukar damuwa kan wannan lamarin na baya-bayan nan

Kwamandan sojojin Amurka karkashin kungiyar Nato a Afghanistan ya nemi afuwa bayan zanga-zangar da aka yi kan rahotannin da ke cewa sojojin kasashen waje "sun zuba takardun alkur'ani a shara.

A wata sanarwa da aka fitar, Janaral John R Allen ya umarci da a gudanar da cikakken bincike.

"Lokacin da muka samu wannan labarin, nan take muka shiga tsakani, sannan muka dakatar da su," a cewarsa.

Rahotannin da aka yada na cewa an kona alkur'ani ya haifar da zanga-zanga a wajen sansanin sojin Amurka a Bagram.

'Yan sanda sun shaida wa BBC cewa akalla mutane 1,000 ne suka shiga zanga-zangar, yayin da wasu dattawan yankin suka shiga sansanin domin tattaunawa da dakarun Nato.

Jami'an Afghanistan sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na AP cewa, an ga Alkur'ani a wata shara da wasu sojojin Amurka biyu suka kai wurin da ake kona bola ranar Litinin da daddare.

Lokacin da 'yan Afghanistan biyu da ke aiki a wurin suka gano Alkur'anin, sai suka dakatar da shirin zubar da sharar.

Wani wakilin BBC a wurin ya ce ya ga mutane suna kuka kan zargin cewa dakarun kasashen waje sun kona Al'kur'ani, yayin da wasu ke jifan dakarun tsaro da duwatsu.

Rahotanni sun ce masu gadi a wurin sun yi amfani da harsashen roba kan masu zanga-zangar da ke kiran "Allahu akbar, Allahu akbar".

'Neman gafara'

A sanarwar da ya fitar, Janaral Allen ya ce binciken zai gano ko sojoji a Bagram "sun zubar da takardu da suka hada da Alkur'ani ta hanyar da bata dace ba".

"Muna gudanar da cikakken bincike, domin tabbatar da cewa hakan bai kara faruwa a nan gaba ba. Ina baku tabbaci....Na yi muku alkawari...wannan ko kadan bai dace da halayyar kasashen duniya ba."

Janar Allen ya kuma "nemi gafara" kan duk abinda hakan ka iya haifarwa ga shugaban Afghanistan, da gwamnatin kasar da kuma "kyawawan mutane Afghanistan".

Masu aiko da rahatanni sun ce sakon janar din wanda aka rinka watsawa a gidan talabijin na Afghanistan - domin rage illar da hakan ka iya haifarwa - saboda a baya irin wannan lamarin ya haifar da hare-hare kan 'yan kasashen waje.

Akalla ma'aikatan Majalisar Dinkin Duniya 10 aka kashe sannan aka raunata wasu da dama sakamakon zanga-zangar da aka yi bayan da wani Fasto ya kona Alkur'ani a jihar Florida ta Amurka.

Karin bayani