An baiwa Girka sabon rance

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tutar kasar Girka

Ministocin kudi na kasashen da ke amfani da kudin bai-daya na euro sun amince da wani sabon shiri da zai baiwa kasar Girka karin tallafi domin shawo kan tabarbarewar tattalin arzikin da ta ke a ciki.

A karkashin shirin dai za a baiwa kasar ta Girka rancen sama da dala biliyan dari da saba'in, yayin da ita kuma za ta rage basussukan da ake bin ta zuwa adadin da bai haura kashi dari da ashirin da daya na arzikin da take samarwa a cikin gida ba.

Hakan na nufin gwamnatin Girka za ta rage kashe kudade fiye da yadda ta tsara a baya, da kuma rage adadin kudin da za ta biya bankunan da suka ba ta bashi.

Ministocin sun bukaci kasar ta Girka da ta rika biyan bashin a hankali zuwa abin da bai haura kashi 120 na tattalinta ba, a cikin shekaru takwas masu zuwa.

An gamsu da matakan da Girka ke dauka

Shugabar Asusun Ba da Lamuni na Duniya IMF, Chirtine Lagarde, ta ce ta gamsu da matakan da kasar ta Girka ke dauka don fita daga kangin tatalin arzikin da take ciki.

Ta ce:''A fili ta ce cewa Girka ta dauki kwararan matakai, don haka ya kamata dukkan bangagorin da suke bin ta bashi su ci gaba da hada kai da ita don ganin ta iya biyan bashin da ke kan ta.IMF ma a shirye take ta hada kai domin dai a gudu tare, a tsira tare''.

Sai dai ba anan gizo ya ke saka ba, domin kuwa ministocin sun dauki wadanda matakai da fatan tattalin arzikin kasar ta Girka zai rika bunkasa.

Don haka idan har Girka ta ci gaba da fuskantar koma-baya a fannin tattalin arzikinta, hakan na nufin wadannan matakai za su fada halin tsaka mai-wuya.

Hakan ne ma ya sanya kasashe irinsu Jamus da Netherlands ke nuna adawarsu da daukar wadannan matakai.

Netherlands ta ce ya kamata a nada wani wakili na dindindin wanda zai tare a birnin Athens, kana ya rika sanya ido kan adadin kudin da gwamnatin kasar ke samu, da kuma yadda take kashe su.

Sai dai wata kungiyar kare hakkin masu sayen kayyaki ta kasar Girka ta yi kira ga 'yan kasar da su daina sayen kayayyakin da kasashen Jamus da Netherlands ke samarwa don nuna bijirewarsu ga adawar da kasashen biyu ke yi a yunkurin da ake wajen ceto tattalin arzikin kasar ta Girka.

Karin bayani