Tashin hankali ya shafi zaben Yemen

Zabe a Yemen Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Zabe a Yemen

Wasu 'yan bindiga sun kashe sojoji akalla takwas a rumfunan zabe a kasar Yemen, inda ake gudanar da zaben shugaban kasa.

Ana zaben ne don maye gurbin Ali Abdullah Saleh.

Tashin hankalin ya biyo bayan kiran da 'yan - a - ware suka yi a Kudancin Yemen a kan a kaurace ma zaben.

An dai rufe rabin rumfunan zabe a birnin Aden, sai dai an gudanar da zabe lami lafiya a Sana'a babban birnin kasar

Mataimakin shugaban kasar Yemen, Abdu Rabbu Mansour Hadi shi ne 'dan takara daya tilo a cikin zaben.

Shugaba Saleh. wanda ya yi shekaru talatin da uku kan mulki ya amince ya sauka bayan watannin da aka shafe ana ta gudanar da zanga zangar nuna rashin amincewa da mulkinsa

Karin bayani