David Cameron ya damu da aikace- aikacen Kungiyar Al Shabab

Firayim Ministan Burtaniya David Cameron
Image caption Firayim Ministan Burtaniya David Cameron ya nuna matukar damuwa dangane da aikace- aikacen Kungiyar Al Shabab

Firayim Ministan Burtaniya David Cameron ya shaidawa BBC cewar aikace- aikacen Kungiyar nan ta masu tsattsauran ra'ayin Islama a Somalia shine babban abinda ke damunsa dangane da Kasar.

A wata hira da Sashen Somali na BBC, Firayim Ministan Burtaniyan ya ce a bayyane take irin barazanar da Kungiyar wadda ke iko da mafi rinjayen Somalia watau Al Shabab ta ke yi ga sha'anin tsaro a duniya.

Yace ya damu da irin yadda ake mayar da matasa 'yan Kasar ta Somalia dake Burtaniya masu tsattsauran ra'ayi, ake kuma daukar su a matsayin mayaka a Kungiyar ta Al-shabab.

David Cameron din ya kuma ce wannan wata babbar barazana ce ga duniya.

Gwamnatin Burtaniyan dai na shirin karbar bakwancin wani babban taro na Kasashen duniya da aka shirya gudanarwa kan Kasar ta Somalia ranar alhamis a birnin Landan.

Karin bayani