Jami'an Iran sun ki bamu hadin kai- IAEA

Jami'an hukumar IAEA a Iran Hakkin mallakar hoto Getty

Hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA ta ce jami'ai a Kasar Iran sun hana wakilan hukumar duba wani yanki da ake kera makaman yaki, a wani bangare na aikin da suke yi na bincikar shirin nukiliya na Kasar.

Wani jami'in hukumar kula da makamashin nukiliyar ya ce, an shafe kwanaki biyu kenan ana neman shawo kan jami'an Kasar su bari a duba wani sansanin soji dake Parchin mai nisan kilomita kamar 30 a kudu maso gabashin Tehran, amma an gaza daidaitawa.

Daraktan hukumar kula da makamashin nukiliyar Yukiyo Amano ya ce bai ji dadi ba da Kasar ta Iran ta ki yarda da bukatar hukumar sa.

Karin bayani