Amurka na shirin daukar karin matakai akan Syria

Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Akwai yiwuwar Amurka ta kara daukar matakai akan Syria

Amurka ta gargadi Syria ga abinda ta kira karin wasu matakai, idan har Shugaba Assad ya ki kawo karshen hare-haren da sojojinsa ke kai wa mutanen Kasar.

Fadar gwamnatin Amurkan da ma'aikatar harkokin wajen Kasar sun ce ba sa son kara dagula al'amura ta hanyar daukar matakan soji a kan Syrian, to amma sun ce ba a yanke kauna ba a kan daukar wasu karin matakai.

Tun farko dai, 'yan adawa masu fafutuka sun bayyana cewar sojojin Syriar sun kashe fiye da mutane dari a wasu munanan hare-hare da suka rinka kaiwa a biranen Homs da Idlib a lardin arewacin Kasar.

Karin bayani