Obama ya nemi afuwa kan batun kona Alkur'ani

An zargi sojojin Amurka da kona Alkur'ani Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sojojin Amurka sun nuna matukar damuwa kan wannan lamarin na baya-bayan nan

Shugaban Amurka Barack Obama ya nemi afuwa daga gwamnatin Afghanistan bayan wasu sojojin Amurkar a kasar sun kona Alkur'ani Alkur'ani mai girma a babban sansaninsu na Bagram abinda ya haifar da zanga-zanga.

'Yan Afghanistan akalla shida da kuma sojojin kungiyar tsaro ta NATO biyu aka kashe a rana ta uku ta zanga-zangar da ake gudanarwa.

Jami'an kasar sun ce an yi wani mummunan bore, inda masu zanga-zanga suka afkawa wani sansanin sojin hadin guiwa tsakanin Amurka da Afghanistan dake gabashin lardin Nangahar.

Haka kuma jami'an sun bayyana cewa wani sojin Afghanistan ya bude wuta kan dakarun kasashen waje dake sansanin. Kuma kungiyar tsaro ta NATO ta tabbatar da mutuwar sojojinta biyu, yayin da kuma a musayar wutar data biyo baya aka kashe mutane biyu daga cikin masu zanga-zangar.

'Ramuwar gayya'

Gidan talabijin din kasar ya nuna hoton bidiyo, inda dakarun kasar ke harba bindiga don tarwatsa masu boren.

Wasu masu zanga-zanga sun kai hari a sansanin sojin Faransa dake birnin Kabul.

An dai samu taho-mu-gama a wasu birane biyu da ke gabashin kasar bayan gungun mutane dake rera waka suna cewa "Allah ya hallaka Amurka" ke jifa da duwatsu, suna kuma fasa tagogi da kona tutar Amurka, inda a nasu bangaren su kuma 'yan sanda suke harbin iska.

Kungiyar Taliban dai ta yi kira da cewa mutanen Afghanistan "su kashe tare da yiwa 'yan kasashen yamma dake kasar duka" a matsayin ramuwar gayya na kona Al'kurani mai tsarkin da suka yi.

Shugaban kasar, Hamid Karzai ya kira wata tattaunawa da 'yan siyasa da shugabannin kabilu a wani yunkuri na yayyafawa lamarin ruwa.

Sai dai da dama daga cikin jami'an kasar na goyon bayan boren da Amurka ta janyo.

'Neman gafara'

A sanarwar da ya fitar ranar Talata, Janaral Allen ya ce binciken zai gano ko sojoji a Bagram "sun zubar da takardu da suka hada da Alkur'ani ta hanyar da bata dace ba".

"Muna gudanar da cikakken bincike, domin tabbatar da cewa hakan bai kara faruwa a nan gaba ba. Ina baku tabbaci....Na yi muku alkawari...wannan ko kadan bai dace da halayyar kasashen duniya ba."

Janar Allen ya kuma "nemi gafara" kan duk abinda hakan ka iya haifarwa ga shugaban Afghanistan, da gwamnatin kasar da kuma "kyawawan mutane Afghanistan".

Masu aiko da rahatanni sun ce sakon janar din wanda aka rinka watsawa a gidan talabijin na Afghanistan - domin rage illar da hakan ka iya haifarwa - saboda a baya irin wannan lamarin ya haifar da hare-hare kan 'yan kasashen waje.

Akalla ma'aikatan Majalisar Dinkin Duniya 10 aka kashe sannan aka raunata wasu da dama sakamakon zanga-zangar da aka yi bayan da wani Fasto ya kona Alkur'ani a jihar Florida ta Amurka.

Karin bayani