An kai hari kan wata makaranta a Maiduguri

Maiduguri Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A yanzu yara da yawa sun kauracewa makarantunsu

Rahotanni daga Maiduguri a Arewacin Najeriya sun ce wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hari a wata makarantar Firamare inda suka cinnawa wasu dakunan karatun wuta.

A kwanaki ukun da suka gabata ma an kai irin wannan hari a makarantar Firamare ta Kolugumna dake birnin.

Hukumomin sunce an tafka asarar wasu gine gine da kayan karatu, sai dai ba a samu asarar rayuka ba.

An kuma bada rahoton cewar 'yan makarantar da abin ya shafa da dama sun kauracewa makarantun nasu sakamakon abkuwar lamarin.

Wannan hari da 'yan bindigar suka fara kaiwa makarantun Firamaren a Maiduguri wani abune ne da za a iya cewa na ba kasafai ba a cikin irin jerin hare-haren da aka dade ana fama dasu a birnin.

Farfesa Tijjani Abba Ari kwamishinan Hukumar Bayar da Ilmin Firamare bai daya UBE a jihar ta Borno, ya shaida wa BBC cewa harin ya lalata kayayyakni aiki da dama a makarantar, amma babu asarar rayuka.

Yara da dama ne suka kauracewa makarantun nasu sakamakon wannan harin, kuma wakiliyar BBC Bilkisu Babangida a Abuja, ta ce lamarin ka iya gurgunta harkokin karatun nasu idan ba mahukuntan sun dau matakai ba.

Karin bayani