Gloria Arroyo ta ki amsa laifin tafka magudin zabe

Tsohuwar Shugabar Philippines Gloria Arroyo Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana zargin Gloria Arroyo da tafka magudin zabe a shekarar 2007

Tsohuwar Shugaba a Kasar Philippines Gloria Arroyo ta ce ba ta da laifi a cajin da aka yi ma ta na tafka magudin zabe a lokacin da ta bayyana a gaban wata Kotu dake birnin Manila.

Mrs. Arroyo wadda ta shugabanci Kasar har na tsawon shekaru 9, an zarge ta da laifin hada baki a dagula sakamakon zabe don mara wa wasu 'yan takara baya, a zaben kananan hukumomin da aka yi a shekara ta dubu biyu da bakwai.

Masu gabatar da kara sun zargi Mrs. Arroyo wacce aka kame a cikin watan Nuwamba da laifin taimaka wa wani jagoran mayaka a murdiyar zaben majalisar dattawa.

Mrs. Arroyo dai ta musanta wannan zargi na yin abinda ya saba wa doka, tana mai cewar Magajiyar ta ce Benigno Aquino ke neman shafa ma ta kashin-kaji.

Za a dai iya yanke ma ta hukuncin daurin rai-da-rai idan aka same ta da laifi.

Karin bayani