An cimma matsaya a taro kan makomar Somalia

Kasar Somalia Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugabannin gwamnatin rikon kasar sun halarci taron, amma banda kungiyar Al shabab

Fira ministan Burtaniya David Cameron ya ce an cimma matsaya kan batutuwan da suka shafi tsaro da fashin jiragen ruwa da ayyukan jinkai a taron da aka gudanar kan makomar kasar Somalia a birnin London.

Mr Cameron na magana ne a lokacin da yake rufe taron na kasa da kasa da aka shirya kan kasar ta Somalia.

Taron ya samu halartar wakilai daga kasashe 40 ciki harda Najeriya wacce ita ma ke fama da natsalar kungiyar Boko Haram - makamanciyar ta Alshabab a Somalia.

Wakilai daga kasashe 40 ne ke halartar taron, domin bayar da shawara kan yadda za a fuskanci matsalolin da ke addabar kasar wacce ta shafe shekaru da dama cikin yakin basasa da matsalar karancin abinci.

Masu sharhi da dama dai na nuna shakku kan yadda wannan taron zai yi tasiri wajen shawo kan matsalolin da 'yan kasar ta Somalia ke fama da su.

Tunda farko dai Burtaniya ta bayyana Somalia a matsayin "kasar da ta fi kowacce rashin tabbas a duniya" amma ta ce a kwai bukatar a sake bata dama.

Al Shabab ba za ta halarta ba

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton, ta ce Amurka ba za ta taba tattaunawa da kungiyar ta Al shabab ba, amma kuma ta ce a shirye kasar ta ke ta yi aiki da kungiyoyin da suka nuna sha'awar ci gaban kasar ta Somalia.

Wakilai na gwamnatin rikon-kwaryar kasdar da Kungiyoyi daban-daban sun halarci taron, amma banda Kungiyar 'yan gwagwarmaya ta Al Shabab wadda ke da ikon mafi rinjayen tsakiya da kuma kudancin Kasar ta Somalia.

Al shabab ta bayyana taron da cewa mani yunkuri ne na sake mamaye Somalia, sannan ta yi Allah wadai da duk wani mataki da za a dauka a wurin ta mai cewa "ba zai yi tasiri ba".

Wannan wani yunkuri ne da Firayim Ministan Burtaniya David Cameron ke jagoranta don nemo sabbin hanyoyin da za a kawo karshen yamutsi da yunwa da yakin basasar da aka shafe sama da shekaru ashirin ana gwabzawa a Kasar.

A waje daya kuma dakarun Habasha da taimakon sojan gwamnatin rikon kwaryar Somalia sun kwace ikon mulki da birnin Baidoa dake tsakiyar Kasar a hannun mayaka na Kungiyar Kishin Islama ta AlShabab.

Sun kwaci birnin ne salun-alun ba tare da wani fada ba lokacin da mayakan na Al Shabab suka arce daga yankin suna cewar maimakon fadan, za su koma yakin sari-ka-noke

To amma masu aiko da rahotanni sun ce hakan wani babban koma-baya ne ga Kungiyar ta AlShabab.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Karin bayani