An tsegunta sunayen wadanda za a iya tuhuma da laifin yaki a Syria

Birnin Homs Hakkin mallakar hoto Other
Image caption Birnin Homs

Majalisar dinkin Duniya ta fitar da jerin sunaye na sirri a kan jami'an sojin Syria da aka yi amana, ciki har da shugaba Bashar Assad, wadanda mai yiwuwa su fuskanci bincike kan toye hakkin bil-adama.

Wani sabon rahoto na masana hakkin bil-adama, wanda Majalisar Dinkin Duniyar ta kafa ya nuna cewa akwai kwakkwarar shaida a kan shugabannin soji da kuma na gwamnati game da toye hakkin bil-adama.

Paulo Pinheiro shi ne jagoran kwamitin bincike kan kasar Syria na Majalisar Dinkin Duniyar.

Ya ce, “Lamarin ya kara muni sosai ta yadda muna samun karin sheda a kan abin da ke faruwa.

“Mun samu bayanai da shedu, kuma mun tattauna da wadanda ba sa goyon bayan gwamnatin kasar.

Karin bayani