An kafa dokar hana fita a Gombe

Jami'an tsaron Najeriya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Hare-haren na zuwa ne duk da matakan da jami'an tsaro suka ce suna dauka

Rahotanni daga Najeriya, na cewar wasu 'yan bindiga sun kai wasu jerin hare-hare a Gombe, babban birnin Jihar Gombe da ke yankin arewa maso Gabashin kasar.

Mazauna birnin na Gombe sun shaida wa BBC cewa sun ji karar fashewar wasu abubuwa da ake kyautata zaton bama-bamai ne.

Wasu rahotannin sun ce an kai harin ne wani gidan kaso da ke birnin da kuma wani caji ofis na 'yan sanda hari.

Mazauna birnin sun ce an shafe sa'o'i ana jin karar fashewar abubuwan da kuma harbe-harben bindigogi.

An bude wuta kan masallata

Rahotanni daga Jihar Kano na cewa wasu 'yan binduga sun bude wuta akan wasu suna idar da sallar Magariba inda harin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane hudu mutun daya ya ji rauni.

Harin ya faru ne a ungwar Sallari a birnin na Kano, hukumomin 'yan sanda sun tabbatar da afkuwar lamarin.

Wannan ne karo na farko da birnin na Gombe ke fuskantar irin wannan mummunan harin.

Kawo yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin hare-haren, sai dai sun yi kama da irin wanda kungiyar Boko Haram ke kaiwa a Najeriyar.

Wani hari makamancin wannan da kungiyar ta kai a jihar Kano a kwanakin da ya gabata, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kusan 200.

Yankin Kudu maso Gabashin kasar nan ne dai hedkwatar kungiyar ta Boko Haram, amma a 'yan kwanakin nan, kungiyar na fadada ayyukanta zuwa wasu sassan kasar.

Ita dai Boko Haram tana yaki da jami'an tsaron Najeriya, domin yunkurin kafa tsarin shari'ar Musulunci a wasu sassan Najeriya.

Sai dai 'yan kasar da dama ba sa goyon bayan yadda kungiyar ke gudanar da al'amuranta.

Karin bayani