Firaministan Rasha ya zargi kasashen yamma da shirin far wa Iran

Firaminista Vladimir Putin Hakkin mallakar hoto RIA Novosti
Image caption Firaminista Vladimir Putin

Firaministan Rasha, Vladimir Putin, ya zargi kasashen yammacin duniya da fakewa da fargaba a kan shirin nukiliyar Iran domin kawo sauyin gwamnati a Iran din.

Mista Putin ya ce Rasha ba ta yarda da wannan manufa ba, kuma za ta cigaba da turjewa duk wani yunkuri na yin hakan.

A wani bangaren kuma, hukumar sa ido a kan harkokin nukiliya ta duniya, IAEA, tana samun karin damuwa saboda yiwuwar Iran ta yi amfani da shirinta na nukiliya wajen yin makamai.

Kasashen Yamma dai suna zargin Iran din ne da kokarin kera makaman nukiliya, yayin da ita kuma take cewa shirin nukiliyarta na samar da makamashi ne kawai.

Karin bayani