Dubun- dubatar mutane na tserewa fadan arewacin Mali

Sansanin 'yan gudun hijira a Mali Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana cigaba da samun dubun- dubatar mutanen dake tserewa fadan arewacin Mali

Majalisar dinkin duniya ta ce adadin mutanen da suka guje wa fadan da ake gwabzawa a arewacin Kasar Mali ya haura dubu dari da ashirin.

Kusan dai dukkanin mutanen da su ka tsere sun tsallaka ne zuwa Kasashen makwabta irinsu Mauritania da Nijer da Burkina-Faso.

A watan da ya gabata ne aka fara gwabza fadan a Mali, lokacin da mayakan buzaye suka hada kai da gungun wasu 'yan tawaye, su ka rinka kai hare-hare a garuruwan dake arewacin Kasar da sansanonin soji.

Kawo yanzu dai, babu wata majiya mai zaman kan ta da ta tantance yawan mutanen da aka kashe a fadan.

Karin bayani