Mutane 130,000 ne suka tserewa rikicin Mali

Mutane 130,000 ne suka tserewa rikicin Mali Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan gudun hijirar an matukar bukatar taimakao

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin mutane 130,000 ne suka bar gidajensu sakamakon fadan da ake gwabzawa tsakanin 'yan tawayen Abzinawa da dakarun gwamnati tun watan Janairu a kasar Mali.

Fadan ya raba mutane 60,000 da gidajensu a cikin Mali, yayin da wasu karin 69,000 suka tsallaka zuwa makwaftan kasashe, kamar yadda mai magana da yawun Majalisar ya shaida wa BBC.

Adrian Edwards ya yi gargadin cewa ana bukatar agajin gaggawa, domin 'yan gudun hijirar "ba su da komai".

Jama'a da dama sun rasa rayukansu, amma babu cikakkun bayanai.

Kungiyar Azawad National Liberation Movement (MNLA), wacce ke neman samun kasar Abzinawa a Arewacin Mali, ta kaddamar da hare-hare ne a watan da ya gabata, inda ta ke kai hare-hare kan birane da sansanonin soji.

Wannan ya zo ne bayan da mayakan Abzinawa da dama da suka yi yaki tare da magoyan bayan Kanal Gaddafi suka koma daga Libya.

Kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun yi kira ga gwamnati kada ta kai hare-hare kan fararen hula.

'Matukar bukatar taimako'

Sake barkewar fadan ta zo ne bayan shafe shekaru biyu ana zaman lafiya tsakanin gwamnati da Abzinawa.

"Cikin 'yan makwannin da suka wuce, an raba dubban jama'a da gidajensu inda suka tafi gudun hijira zuwa akalla kasashe hudu da ke makwaftaka da Mali," a cewar Mr Edwards.

Ya kara da cewa akwai akalla mutane 60,000 a cikin Mali, tare da wasu 29,000 a Nijar, 22,000 a Mauritania da kuma 18,000 a Burkina Faso.

Mutane 130,000 da aka kiyasta sun tsere sakamakon rikicin sun kai kashi 0.8% cikin dari na baki dayan jama'ar Mali.

Mr Edwards ya yi gargadin cewa suna cikin "matukar bukatar" kayan abinci - ciki harda matsuguni da abinci da ruwan sha da kuma magunguna.

Karin bayani