Zabe a Senegal babu gudu ba- ja- da- baya- N'Diaye

Abdoullaye Wade na Senegal Hakkin mallakar hoto
Image caption 'Yan adawa a Senegal sun nemi Abdoullaye Wade ya sauka daga kan mulki

Firayim Ministan Kasar Senegal Sulaiman Ndene N'Diaye ya ce za a yi zaben Shugaban Kasar kamar yadda aka tsara a ranar lahadi.

Wasu kungiyoyin 'yan adawa sun nemi a dage zaben, sun kuma lashi takobin cewar za su sanya komai ya tsaya cik a Kasar idan har Shugaban Kasar Abdullahi Wade mai shekaru tamanin da biyar da haihuwa ya ki sauka daga kan mulki.

Yana takara ne karo na ukku sabanin wa'adi biyu da tsarin mulkin ya tanadar a Kasar.

Tsohon Shugaban Najeriya chief Olusegun Obasanjo yana ganawa da shugabannin 'yan adawar da suka hada da sanannen mawakin nan Yousuf Ndor, a kokarin sassauta zaman zullumin da ake ciki.

Karin bayani