Kungiyar agaji ta Red Cross ta sami shiga birnin Homs na Syria

Birnin Homs Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Birnin Homs

Kungiyar agaji ta Red Cross da kuma bangarenta na Syria yanzu haka suna birnin Homs na Syriar, inda suke tattaunawa da hukumomin birnin da kuma dakarun 'yan adawa domin fitar da wadanda suka jikkata kuma ke matukar bukatar kulawa.

Ba a dai bada karin bayani ba a kan hakan:

Wakiliyar BBC ta ce, “Kungiyar agajin ta Red Cross dai ba ta ba da cikakken bayani ba a kan lokacin da za ta soma kwashe wadanda suka jikkata daga birnin na Homs.

Yanzu haka dai akwai 'yan Syria da dama da kuma wasu 'yan jaridar kasashen yamma da ke matukar bukatar agaji.

Hakan tana aukuwa ne byan da sojin gwamnatin Syriar suka kwashe makonni suka luguden wuta a kan birnin na Homs, inda suke fuskantar turjiya daga masu fafitika.

Karin bayani