An kashe jami'an tsaron NATO a Afghanistan

Image caption Qur'anan da aka ce an kona a Afghanistan

Kungiyar tsaro ta NATO a Afghanistan ta ce an kashe wasu dakarun ta 2 a wata musayar wuta da suka yi a cikin ginin ma'aikatar cikin gida dake birnin Kabul.

An yi imanin cewa mamatan , sojojin Amurka ne.

Tuni dai aka killace yankin, amma har yanzu ba'a san wanda ya fara bude wuta ba.

Wannan al'ammari dai na faruwa a dadai lokacin da ake cigaba da mummunar zanga-zanga a rana ta biyar a jere a kasar ta Afghanistan, a kan batun kona alkura'ani mai girma a wani sansanin sojan Amurka dake kasar.

Rahotanni sun ce akalla mutane 7 sun hallaka, wasu karin 60 kuma suka samu raunika a arangamar da aka yi tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zangar.

Akalla mutane 25 ne suka rasa rayikansu a zanga-zangar da aka yi a cikin wannan makon, ciki har da sojojin Amurka 2.

Karin bayani