Taliban ce ta kashe sojin NATO biyu a Afghanistan

Masu zanga zanga a Afghanistan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu zanga zanga a Afghanistan

Wani dan bindiga ya hallaka wasu manyan jami'ai masu bada shawara na kungiyar NATO su 2 a cikin harabar ginin ma'aikatar harkokin cikin gidan Afghanistan mai cike da tsaro a Kabul, babban birnin kasar.

An yi imanin cewa mamatan Amurkawa da suka hada da Kanar guda da kuma wani Manjo.

An kashe su ne a Cibiyar bada umarni ta NATO dake cikin ginin ma'aikatar, kuma rahotanni sun ce maharin ya arce.

Birgadia Janar Carsten Jacobson,kakakin rundinar ISAF ya tabbatar cewa ma'aikatan rundinar ISAF biyu sun hallaka a wannan al'ammari.

Hakkika wannan wani abun bakin ciki ne, kuma za'a gudanar da bincike a kai.

Kungiyar Taliban dai ta ce ita takai wannan hari, don daukan fansa a kan yadda aka kona alkura'ani mai girma a wani sansanin sojan Amurka a makon jiya.

Karin bayani