Shin za a bukaci kafafen yada labarai anan gaba?

Shafukan sada zumunta Hakkin mallakar hoto COLLAGE
Image caption Shafukan sada zumunta na taka muhimmiyar rawa wurin yada labarai a duniya

Babu shakka shafukan sada zumunta kamar Facebook, Twitter da You Tube sun sauya yadda muke samun labarai.

Shafukan sada zumunta sun yi matukar sauya yadda kafafen yada labarai na duniya ke gudanar da ayyukansu.

A lokacin wani taro da BBC ta shirya bara kan shafukan sada zumunta, manajan editan jaridar Washington Post ya yi wani jawabi mai daukar hankali inda ya ce "Mai zai sa na dauki dan jaridar da bashi da adreshin Facebook ko Twitter?"

Tuni aka fara tattaunawa kan ko nan gaba za a bukaci kafafen yada labarai kamar rediyo da talabijin.

Amsar ita ce kamata ya yi a koma a duba tarihin yadda fasaha ke habbaka.

Alakar lamarin da tarihi

Idan muka duba tarihin gidajen buga takardu a shekarun 1400, amfani da allunan buga takardu a 1700, da tarho a 1800, da kuma rediyo a 1800 zuwa farkon 1900, sun ci karo da mulkin mallaka da kuma yakin duniya.

Lokacin da aka kirkiro kowanne daga cikin wadannan, mutane sun yi hasashen cewa mafi sabunta daga cikin zai maye gurbin sauran.

Lokacin da aka fara amfani da tauraran dan'adam a 1980, an nuna damuwa kan cewa zai kawo karshen jaridu.

Duk da cewa tauraron dan'adam ya sauya yadda jaridu suke aiki, amma har yanzu suna aiki duk da cewa suna fuskantar wani yanayi mai tsauri.

Al'umma a duniyar gizo mai cibiya a kan nau'ra mai kwakwalwa

Idan aka yi la'akari da shafukan sada zumunta kamar Twitter da Facebook, wani sauyi ne aka samu ta fannin fasaha wanda kamar rediyo da talabijin sun karo da wasu abubuwan na zamani.

Mafi muhimmanci shi ne boren kasashen Larabawa wanda ya kai ga kifar da gwamnatocin kasashen Tunisia da Masar da kuma Libya. Ya kuma yi tasiri a Wall Street a Amurka da Turai da ma Afrika.

Wannan tasiri ya kuma sauya fagen siyasan duniya inda jama'ar da ke amfani da facebook suka suka ninka adadin yawan jama'ar Amurka.

Wannan shi ne abinda zan kira kasashen da suka yi nisa wurin amfani da kafofin sadarwa na zamani.

Suna cike da matasa wadanda koda yaushe suna tare da na'urorin kwamfiyuta da kuma wayoyin na salula masu komai-da-ruwanka.

Sun riga sun saba da amfani da irin wadannan kayayyakin fasaha na zamani; don haka kalubalen da ke gaban kafafen yada labarai na zamani shi ne su shiga a dama da su a wannan fagen.

Image caption Internet da shafukan sada zumunta sun taka rawa a boren Kasashen Larabawa

Nan da shekaru masu zuwa, wadannan matasan ne za su zamo masu fada aji, haka kuma masu shiryawa da kuma sauraran labarai.

Ban amince da batun da ake na cewa shafukan sada zumunta ko kuma internet, za su maye gurbin talabijin da rediyo kwata-kwata ba. Abinda zai faru shi ne za su sauya yadda ake gudanar da harkokin watsa labarai.

Tuni mun fara ganin gidajen talabijin a Amurka kamar PJTV duk da kayan aikin da suke da su irin na zamani, amma suna watsa shirye-shiryen na su kawai a internet.

Nan gaba za a samu karin kafafen yada labarai da za su bi sahun PJTV, amma ba ruwansu da kalubalen da ainahin gidajen yada labarai za su fuskanta ba.

Karfafa danganta

Sai dai akwai abubuwa masu kayatarwa da talabijin ke samarwa musamman a tsakanin masu matsakaicin hali. Tana kyautata dangantaka tsakanin iyalai, kuma wannan shi ne abinda shafukan sada zumunta ba sa samarwa cikin sauki.

An fi amfani da su ta wayoyin salula domin debe kewa a gida ko makarantu ko kuma wuraren aiki.

Sai dai a wuraren jama'a da dama a kasashe masu tasowa, rediyo na gudanar da makamancin wannan a yankunan karkara.

Za a dauki tsawon lokaci kafin shafukan sada zumunta su maye gurbin tasirin rediyo musamman a inda rediyon ta kasance hanya daya tilo ta samun bayanai.

Wani abu da ya fito fili shi ne lokacin da manyan kafafen yada labarai ke da iko a kan labarai ta wuce, amma hanyar gudanar da cikakken tsarin aikin jarida na nan har gobe.

Kuma wannan shi ne muhimmin abu da ya rage ga 'yan jarida, kuma wata rana masu amfani da hanyoyin sadarwa na zamani za su so su shiga wannan fagen.

Koma dai yaya ta kaya, a yanzu muna karnin shafukan sada zumunta!

Muhammad Jameel Yusha'u

Malami ne a jami'ar Nothurmbria a Burtaniya

Karin bayani