James Ibori 'ya saci miliyoyin daloli'

James Ibori
Image caption Tuni kotu ta samu lauyansa da budurwarsa da kuma matarsa da laifi

Tsohon gwamnan Jihar Delta a Najeriya, James Ibori, ya amsa laifi a gaban wata kotu a London, bisa jerin tuhume- tuhume goma da ake yi masa na kokarin salwanta kudaden haram, da kuma hada baki domin tafka zamba.

'Yan sanda a Burtaniya sun tuhume shi da sace dala miliyan 250 a cikin shekaru takwas.

ames Iborin, wanda a can baya wata kotu a Najeriya ta wanke shi bisa tuhumar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ke yi masa, ya amsa laifin-nasa ne a lokacin da aka zo bude shari'ar a London.

Mr Ibori, wanda a wani lokacin ake yiwa kallon daya daga cikin mafi arziki da karfin fada aji a jam'iyyar PDP mai mulkin kasar, an kama shi ne a shekara ta 2007.

Amma daga bisani aka sake shi, kafin a sake kama shi a Dubai bayan da Burtaniya ta bayar da sammacinsa, sannan aka mika mata shi.

A can baya dai ya tsaya kai da fata akan cewar bashi da laifi, yana mai cewar tuhumar da ake yi masa ta na da nasaba da siyasa.

'Kwace dukkan dukiyar da ya sata'

Za a yanke masa hukunci a ranar 16 ga watan Afrilu.

Tuni kotu ta yankewa matarsa Theresa, 'yar uwarsa, Christine, farkarsa, Udoamaaka Okoronkwo, da kuma lauyansa a London, Bhadresh Gohil, hukunci kan halatta kudaden haram.

Wakilin BBC Chris Summers, wanda ya halarci zaman kotun, ya ce an samu damar bada labarin amsa laifin na sa ne bayan da aka janye haramcin daukar rahotannin da aka sanya a kotun.

Hukumar yaki da cinhanci da rahsawa a Najeriya (EFCC) ta nemi 'yan sanda a Burtaniya da su duba harkokin kudi na tsohon gwamnan.

"An yi amfani da yawancin kudaden ne wajen daukar nauyin bushashar da tsohon gwamnan ya rinka yi," a cewar jami'in da ke gudanar da bincike Paul Whatmore.

"A yanzu za mu nemi a kwace dukkan dukiyar da ya sata domin a mayar da ita don amfanar jama'ar jihar Delta."

Ya ce kudaden da Mr Ibori ya sata kamata ya yi ayi amfani da su wajen samar da wutar lantarki da inganta harkokin lafiya a kasar da ake fama da matsanancin talauci.

Wata kotu a Burtaniya ta bayar da umarnin rike wasu kadarorinsa a kasar da suka kai na dala miliyan 35.

Albashinsa dai a matsayin gwamnan jihar ta Delta bai kai dala 25,000 ba.

A karkashin tsarin mulkin Najeriya, gwamnonin jihohi na da iko sosai kuma suna kula da kasafin kudi mai dimbin gaske wanda ya haura na wasu kasashen Yammacin Afrika.

Karin bayani