An kashe wani dan sanda a Kaduna

'Yan sandan Najeriya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan sandan Najeriya

Rundunar yan sandan jahar kaduna a Najeriya ta tabbatar da halaka wani dan sanda a yammacin yau tare da raunata wasu karin biyu a kaduna.

Dan sanda na farko dai ya gamu da ajalin sa ne yayin da wasu yan bindiga akan babur suka bi shi, suka kuma bindige shi a unguwar Kakuri.

Sauran yansanda biyu da suka sami raunuka kuma, an harbe su ne a unguwar Rigasa.

Rundunar yansandan jahar ta Kaduna dai ta ce tuni ta fara gudanar da bincikea kan lamarin.

Kisan 'yan sandan dai na zuwa kwana daya bayan wasu jarin hare hare da aka kai a jahohin Gombe da Kano, inda duka aka samu asarar rayuka.

Karin bayani