Sabbin takunkumi kan kasar Syria

Sabbin takunkumi kan kasar Syria Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Yan kasar Syria sun fito domin kada kuri'ar raba-gardama kan kundin tsarin mulki

Kungiyar Tarayyar Turai ta azawa Syria sabbin takunkumi, da suka hada da rike dukkan dukiyar babban bankin Syrian da ke kasashen Tura.

An dai yanke shawarar daukar wannan mataki ne a taron ministocin hulda da kasashen waje na Tarayyar ta Turai.

Masu fafutuka dai na cewa, akalla mutane goma sha takwas ne aka akshe a birni na uku mafi girma, wato Homs.

Dama dai tuni Kungiyar Tarayyar Turan ta azawa kasar ta Syria takunkumi kan hana sayen makamai da danyen manta, kana kuma a yanzu ta kara yunkurawa wajen matsa kaimi, ta hanyar saka takunkumin balaguro kan wasu mutane bakwai masu kusanci da shugaba Assad.

Jiran sakamako

Har ila yau an dakatar da harkokin shige da fice na jiragen samar daukar kaya daga Syria zuwa kashen kungiyar ta Tarayyar Turai harma da kasuwancin zinari da karafuna masu daraja.

Duka wadannan dai ba za su iya kawo wani sauyi cikin sauri ba, amma hakan na nuni da cewar wani salo ne na yunkurin kakaba takunkumin tattalin arziki dana diflomasiyya kan gwamnatin Syria.

Yanzu haka da hare-haren dakarun gwamantin Syriar na ci gaba da faruwa akan birnin Binnish inda 'yan adawa suka fi rinjaye, wanda kuma keda yawan jama'a kusan sama da dubu arba'in.

Ministocin harkokin wajen Tarayyar Turan sun yi watsi da kuri'ar zaben raba-gardamar da aka gudanar kan sabon tsarin mulkin kasar ta Syria a matysayin wani abu maras alfanu.

Yanzu hakan dai 'yan kasar ta Syria da dama na zaman jiran yadda sakamkon zaben raba gardamar zai kasance.

Karin bayani