Yau ake gudanar da babban zabe a Senegal

Hakkin mallakar hoto
Image caption Akwatunan jefa kuri'a a Senegal

A ranar Lahadi ce jama'a ke fita don kada kuri'a a zaben shugaban kasar Senegal mai cike da kace-nace.

Shugabannin duniya sun yi kira a kwantar da hankula yayin da ake kada kuri'a a zaben, wanda Shugaba Abdoulaye Wade ke neman wa'adin mulki na uku.

Shawarar da shugaban mai shekaru tamanin da biyar a duniya ya yanke ta sake tsayawa takara ta haddasa zanga-zanga a kasar.

'Yan adawa sun ce kundin tsarin mulkin kasar ya haramtawa Shugaba Wade tsayawa takara, ikirarin da Mista Wade din ya yi watsi da shi.

A yunkurin kawo karshen ta da jijiyoyin wuya, wakilin Tarayyar Afirka, tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya ba da shawarar cewa Mista Wade ya yi murabus bayan shekaru biyu idan aka sake zabensa:

''Koma dai waye ya lashe zaben, bayan lashe shi akwai bukatar maido da zaman lafiya, da tsaro, a kuma hada kan al'ummar kasar don samun ci gaba''.

Gabanin zaben na yau dai, an gudanar da yakin neman zabe cikin tashe-tashen hankula da rudani.

Kotun kolin kasar ce dai ta yanke hukuncin da ya bar Mista Wade ya yi takara a zaben na yau.

Karin bayani