Firayim Ministar Australia ta yi nasara a zabe

Image caption Julia Gillards

Firayim Ministar Australia, Julia Gillard, ta lashe zaben shugabancin jam'iyar Labour mai mulki, wanda aka yi fafatawa mai zafi tsakaninta da mutumin da ta gada, Kevin Rudd.

Mis Gillard ta samu kuri'u saba'in da daya yayin da Mista Rudd ya tashi da kuri'u talatin da daya.

Mista Rudd, wanda aka tube daga shugabancin jam'iyyar da kuma mukamin Firayim Minista a shekarar 2010, bai taba boye kwadayinsa na sake komawa kan mukamin ba.

Mis Gillard ta ce a yanzu 'yan jam'iyyar Labour sun zama tsintsiya madaurinki daya kuma a shirye suke su lashe babban zaben da za a gudanar badi:

''A baya ma mun sha fafatawa a matsayinmu na jam'iyyar siyasa kamar yadda abokan adawar mu na jam'iyyar Conservative suka sha fafatawa, mun kuma nuna cewa za mu iya dawowa mu hada kai domin dangantakar da ke tsakaninmu ta fi komai karfi''

Karin bayani