Jama'atul Nasril Islam ta nuna damuwa a kan hare-hare a Jos

Taswirar Najeriya
Image caption Taswirar Najeriya

A Najeriya kungiyar jama'atul Nasrul Islam ta nuna damuwa dangane da harin kunar bakin wanken da aka kai a wani coci da ke Jos, babban birnin jahar Filato.

Kungiyar ta jama'atul Nasril Islam, wadda ta kira wani taron manema labarai a yau, ta kuma nuna damuwa dangane da asarar rayukan da aka samu a harin, da kuma kashe-kashen ramuwar gayyar da ya biyo baya.

Kungiyar ta ce saboda haka take ganin bai kamata wasu su dinga daukar doka a hannunsu ba da zarar an sami matsala irin wadda ta auku ta ramuwar gayya a jihar ta Filato.

Sakataren kungiyar ya ce a dinga yin bincike sosai idan aka kai wani hari don tabbatar da gaskiyar wanda ya kai shi don tabbatar da zama lafiya.

Karin bayani